Jam’iyyar APC mai mulki ta ce Najeriya na gab da durkushewa ta fuskar tattalin arziki lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulki a shekarar 2023, tana mai gargadin cewa da ba a ɗauki tsauraran matakai ba, ƙasar na iya rugujewa.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Ya ce: “Mun kasance da zaɓi biyu: ko dai mu bari ƙasa ta rushe, ko kuma mu ɗauki mataki. Mun ci bashin da ya yi yawa, an buga kuɗi ta hanyar da ba ta dace ba har ya kai tiriliyoyin Naira, sannan damar aro kuɗi daga ƙasashen waje ta kusa ƙarewa. Har sai da muka jinginar da man fetur tun kafin a hako shi domin samun rancen da za a kashe wajen kasafin kuɗi. Ƙasa ta kusa tsayawa cak.”
Yilwatda ya kuma kare matakin cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, yana mai cewa mataki ne mai tsauri da aka daɗe ana buƙata.
Ya ce marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tun a shekarar 1984 ya taɓa cewa cire tallafin mai shi ne mafita ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
A cewarsa: “Fiye da shekaru 40 bayan haka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki wannan mataki mai ƙarfi domin kawo sauyin da ake buƙata domin ci gaban ƙasa.”
Ya ƙara da cewa wasu alamu na tattalin arziki sun nuna cewa matakan sauyi da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun fara haifar da ɗa mai ido, ciki har da ƙaruwa a kudaden shiga ga dukkan matakan gwamnati.
