Gwamnatin Kano ta ce kawo yanzu fiye da tsirran bishiyoyi miliyan uku mutanen jihar suka nema domin dasawa a unguwannin su, karkashin shirin gwamnatin na dasa bishiyoyi miliyan 10 a fadin jihar.
Kwamshinan Ma’aikatar Albarkatun ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan lokacin da yake jagorantar dashen tsirran bishiyoyi 500 a fadar Sarkin Kano Muhammad Sanusi II.
Dr Dahiru ya ce sanin muhimmanci da darajar bishiyoyi da yin dashen su ne, ya sanya da kan sa ya bukaci gwamnati da ta dasa masa bishiyoyi 500 a fadar ta sa domin yakar dumamar yanayi da kawata fadar ta sa.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya ce rabon da a samu yanayin zafin gari irin wanda ake fuskanta yanzu musamman a Kano kusan shekaru 40 kenan wanda shima a yankin Borno da Kasar Chadi aka fi samun sa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na bukatar al’ummar Kano da su ci gaba da yin dashen bishiyu da rainon su domin magance barazanar yanayin da duniya ke fuskanta kuma yake barazana lafiya, tattakin arziki da rayuwar al’ummar duniya.
