Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaMajalisa wakilai ta koka kan yadda jami'an tsaro ke kama 'yan jarida...

Majalisa wakilai ta koka kan yadda jami’an tsaro ke kama ‘yan jarida yayin da suke bakin aiki a kasar nan.

Date:

Wannan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa daga Akwa Ibom, Clement Jimbo, ya gabatar kan yadda jami’an tsaro ke cin zarafin ‘yan jarida yayin da suke bakin aiki duk da ‘yancin da kundun tsarin mulki ya basu na gudanar da aikin su.

Clement Jimbo, ya ce jami’an tsaro ne ke kama ‘yan jarida ta hanyar dogaro da laifin cin zarafi ta Internet a cikin dokar hukunta laifuka ta Intanet.

Ya ce a farkon shekarar nan shugaba Tinubu ya amince da gyara dokar laifuka ta Internet Amma duk da haka jami’an tsaro basa amfani da gyaran dokar.

Majalisar wakilan ta bukaci hukumomin tsaron da su rinka martaba ‘yan jarida yayin da suke bakin aiki.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...