Ahmad Hamisu Gwale
Gwamnatin tarayya ta bayyana za a ci gaba da aikin gyaran manyan madatsun ruwan Kano ta Kudu da suka hadar da dam din Challawa na Karaye, da na Tiga da ke Bebeji, da kuma na Kafin Ciri da ke karamar hukumar Garko.
Babbar Sakatariya mai kula da hukumar kare muhalli ta kasa, a ofishin sakataren Gwamnatin tarayya, Dr. Aishetu Gogo ce ta bayyana hakan, bayan ta jagoranci masana, muhalli da masu ruwa da tsaki daga Gwamnatin tarayya sun ziyarci wuraren.
Gogo tace, tuni Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta fara shirin gyaran dam din Challawa Goje, da na Tiga da kuma na Kafinchiri a yunkurin tabbatar da manoma, sun amfana da su domin su ci gaba da yin noma da zai bunkasa tattalin arzikin kasa.
Yunkurin ci gaba da aikin na zuwa ne, bayan Sanatan Kano ta kudu Abdurrahman Kawu Sumaila da wasu masu ruwa da tsaki a jihar Kano, sun bukaci shugaba Tinubu da ya karasa aikin domin amfanar da al’ummar yankin dama kasa baki daya.
Da take ganawa da manema Labarai jim kadan bayan kammala zagayen madatsun ruwan, Dr. Aishetu Gogo, ta bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki a jihar Kano domin samun nasarar aikin.
Ta kuma ce Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta dauki matakin gyaran madatsun ruwan ne, domin kaucewa abin da ya faru a birnin Maiduguri na jihar Borno, na iftilain ambaliyar ruwa sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau.
Gogo, ta kara da cewa ofishin ta mai na kula da muhalli na kasa, na kokarin magance duka wasu matsaloli da suka shafi jihohin kasar nan 36 har da Abuja, a yunkurin magance matsalolin gurbacewar muhalli da ambaliyar ruwa.
Wasu manoman da aka ziyarci yankunansu a ganawarsu da Premier Radio sun bayyana, kammala aikin zai kara bunkasa harkokin noma da suke gudanarwa.
Sun kuma bukaci mahukunta da su yi abin da ya dace, wajen cika alkawarin da suka dauka na kammala aikin cikin kankanin lokaci.
A nasa jawabin Sanatan Kano ta kudu Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce, rashin kammala aikin na daga cikin abin da yake ciwa mazauna Kanu ta kudu tuwo akwarya.
Sai dai ya mika jinjina ga Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya ji kokensu kuma ya bukaci a ci gaba da aikin.
Kawu Sumaila, wanda ya samu wakilicin Aliyu Abubakar Bullet, ya ce dama yankin Kano ta Kudu noma yana daga cikin abin da suka dogara da shi.
Har ma ya bayyana idan aka kammala aikin gyaran manyan madatsun ruwan, harkokin noma za su inganta matuka, wanda hakan zai farfado da tattalin arzikin yankin dama jihar Kano baki daya.