Dakatarwrar za ta fara aiki ne daga Juma’a 31 ga Janairu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Taswirar Filaye da Kasa (KANGIS) na jihar Kano, Dakta Dalhatu Sani Aliyu, ya bayyana cewa sabunta takardun mallakar fili ko gida a jihar Kano an dakatar da shi daga ranar 31 ga Janairu, 2025.
A yayin zantawarsa da manema labarai Dakta Dalhatu ya bayyana cewa, tun daga ranar Juma’a aikin sabunta takardun zai tsaya.
Ya kuma kara da cewa mutane da dama sun bayar da hadin kai tun daga fara aikin, kuma za a fitar da jerin sunayen wadanda suka sabunta takardunsu a hukumar KANGIS.
Wannan dakatarwar ta biyo bayan sanarwar da Kwamishinan Kasa na Kano Alhaji Abduljabbar Umar Muhammad Garko ya bayar a ranar 19 ga Disamba, 2024.
A sanarwar ya jaddada matsayin gwamnatin jihar kan wa’adin sabunta takardun mallakar filayen da gidaje (C-Of-O).