‘Yansanda sun mamaye babban ofishin don kwantaar da wutar rikicin da ya hana taron amintattun jam’iyyar
Rikicin ya barke ne kan kujerar sakataren jam’iyyar na kasa, ya hana gudanar da taron amintattu da ake yi Hedkwatar jam’iyyar na kasa Abuja
A bisa rikicin tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda kowannensu ke ikirarin shi ne Sakataren jam’iyyar na kasa.
Rikicin kuajerar Sakataren ya fara ne lokacin da duk mutanen biyun suka iso taron kwamitin amintattun jam’iyyar da ake gudanarwa a ranar Laraba
Aminiya ta rawaito cewa, a lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan bangarorin biyu.
Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don tsayawa takarar Gwamnan Jihar Imo, takarar da bai yi nasara ba.
A lokacin da ba ya nan, bangaren jam’iyyar na Kudu maso Gabas ya nada Ude-Okoye a matsayin sabon sakataren jam’iyyar.
Amma bayan Anyanwu ya fadi a zaben gwamna, ya yi kokarin karbe kujerarsa a jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa rikici.
A ranar 20 ga watan Disamban 2024, kotun daukaka kara da ke Enugu ta tabbatar da hukuncin wata babbar kotu da ta tube Anyanwu daga kujerar sakataren jam’iyyar, tare da tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakatare.
Jami’an tsaro sun mamaye hedkwatar jam’iyyar don shiga tsakani da kuma kwantar da rikicin dake shirin zama tarzoma.