Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta jihar Kano, KNCDC, ta ce ta kammala shirye-shiryen tunkarar duk wata barazanar barkewar cutar Ebola, bayan tabbatar da shirye-shiryen jami’anta da dakunan gwaje-gwaje na jihar.
Darakta janar na hukumar, farfesa Muhammad Adamu Abbas, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Asabar, inda ya ce hukumar ta dauki matakan da suka dace domin kare lafiyar al’umma.
Farfesa Muhammad Adamu Abbas ya ce sun tabbatar da cewa dakunan gwaje-gwaje nan Kano suna da kayan aikin da ake bukata domin gudanar da bincike idan aka samu zargin kamuwa da cutar.
Ya kuma shawarci al’umma da su gaggauta zuwa asibiti idan suka lura da wasu alamomin rashin lafiya da ba su saba gani ba, maimakon yin sakaci ko jira har sai yanayin ya tsananta.
Wakiliyarmu Halima Ayyuba Adamu ta rawaito cewa Darakta janar din yace an horar da jami’an kula da iyakokin jihar, ciki har da na kan iyakokin kasa, kan yadda za su gano duk wani yanayi da basu saba gani ba, tare da gaggauta sanar da hukumomin lafiya domin daukar matakin da ya dace.
