
Aminu Abdullahi Ibrahim
Jam’iyyar Democrat ta samu rinjaye a majalisar wakilan Amurka, bayan nasarar da ta samu a zaɓen tsakiyar wa’adin shugabancin ƙasar da aka gudanar ranar Talata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu damar karɓe ragamar majalisar, wadda jam’iyyar Republican ta riƙe tun bayan zaɓen shekarar 2022.
A zaɓen, an fafata ne kan kujeru 435 na majalisar wakilan, inda Democrat ke buƙatar ƙarin kujeru biyar domin samun rinjayen.
Wannan nasara na nufin shugaban ‘yan Democrat a majalisar, Hakeem Jeffries, na da damar zama kakakin majalisar idan aka fara sabon zaman majalisar a watan Janairun 2027.
A halin yanzu, wannan sakamakon na nufin gwamnatin Shugaba Donald Trump za ta fuskanci ƙarin ƙalubale wajen aiwatar da wasu manufofinta, musamman idan jam’iyyun adawa suka yi amfani da rinjayen da suka samu wajen sa ido kan ayyukan gwamnati.
Zaɓen tsakiyar wa’adi na Amurka na gudana ne duk bayan shekaru biyu, domin zaɓen dukkan kujerun majalisar wakilai da wasu kujerun majalisar dattawa.
