Gwamnatin jihar Kano ta jadadda kudurinta na marawa kamfanoni masu zaman kansu baya, da suke fafutukar sake fasalin sufuri don saukakawa alumma, tare da cewa kofa a bude take ga duk masu sha’awar zuwa Kano don zuba jari.
Kwamishinan sufuri Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana hakan, a bikin wajen kaddamar da wata cibiyar sauya baburan adaidaita sahu daga masu amfani da Fetur zuwa masu amfani da lantarki wato masu chaji da aka samar anan jihar Kano.
Ya kara da cewa sabuwar fasahar sauya abubuwan hawan za ta kara taimakawa wajen kawo karshen gurbatar yanayi.
Daya daga cikin mamallaka kamfanin na volt Track Africa Bashir Sule ya yiwa Premier Radio karin bayani da cewa sun zo Kano ne don kara saukakawa alumma, kuma hakan zai kara bada damar samar da ayyukan yi ga alumma.
Wannan sabuwar dabara na zuwa ne, yayin da shirin Shugaban kasa Bola Tinubu na amfani da makamashin CNG ya fara karbuwa a wajen alumma, daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da hawa a kasuwar duniya.
