Aƙalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara takwas, bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari ƙauyen Naridon
a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11 na dare ranar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe, sannan suka ƙona gidaje da shaguna.
Sakataren Mai Unguwar Naridon, Dogon Rana, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa wannan shi ne mafi muni da ƙauyen ya taɓa fuskanta.
Ya ce maharan sun kai harin ne lokacin da wasu mazauna ke ci gaba da harkokinsu na dare, yayin da wasu kuma suka riga suka kwanta barci.
Sai dai ya bayyana cewa akwai fargabar adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa saboda yanayin raunukan da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata suka samu.
A cewarsa, ƙauyen Naridon na kan iyaka da wasu yankunan jihar Filato, kuma rashin ingantacciyar hanya zuwa ƙauyen ya hana jami’an agaji isa cikin gaggawa, lamarin da ya ƙara yawan waɗanda suka mutu da kuma wahalar tserewa ga mazauna.
Saboda haka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro su ƙara yawan jami’an tsaro a yankin, tare da gina hanyar mota zuwa ƙauyen.
