Mazauna yankin sun ce maharan sun ɗauki tsawon lokaci a ƙauyukan da abin ya faru, amma wasu mazauna garin sun kashe ƴan bindiga 13 a yayin musayar wuta.
Wani mazauni garin ya ce ƴan bindigar sun shiga Ungushi ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Juma’a, lokacin da mutane ke sallar Juma’a inda suka ajiye babura a gaban masallaci, suka tarwatsa masu ibada, sannan suka shiga cikin garin inda suka kashe mutum biyar.
Ya ce daga nan ne suka fara harbe-harbe daga wurare daban-daban tare da kewaye garin, lamarin da ya tilasta wasu mazauna tserewa zuwa cikin gidaje ko hawa wani tsauni domin tsira.
Ya ce sai da jami’an tsaro suka isa yankin kafin maharan su bar garin.
Sun ce harin ya shafi wasu ƙauyuka da suka haɗa da Umbutu, Maikurhuna, Gwandi, Girkau da Zugu, inda aka sace dabbobi da wasu kayayyaki.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta ce ba ta da cikakken bayani kan adadin waɗanda aka kashe
