Tshisekedi Ya Zargi Kabila Da Zama Wakilin Kagame A Kongo
Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Félix Tshisekedi, ya zargi tsohon shugaban ƙasar, Joseph Kabila, da zama wakilin muradun Shugaban Rwanda, Paul Kagame, wajen rura rikicin da ke faruwa a gabashin ƙasar.
Tshisekedi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ’yan majalisar da ke goyon bayan gwamnatinsa, inda ya yi zargin cewa Kagame ne ya tura Kabila domin jagorantar sabon yunƙurin ’yan tawaye.
Zargin na zuwa ne bayan Kabila ya karɓi jagorancin sabuwar ƙungiyar siyasa da mayaƙa ta FRN, wadda ta haɗa da shugabannin ƙungiyar ’yan tawayen M23.
Sai dai Kabila ya musanta zarge-zargen cin amanar ƙasa da gwamnatin Kongo ke yi masa, yayin da Rwanda ke ci gaba da musanta zargin tallafa wa ’yan tawayen M23.
Rikicin gabashin Kongo ya daɗe yana haddasa asarar rayuka da raba dubban iyalai da muhallansu.
