
Hakan ya biyo bayan faduwar farashin buhun Fulawa amma farashin Burodi bai sauka ba.
Hukumar Karbar Korafe Korafe Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ta yi wani zama na musamman da kungiyar masu burodi don rage farashin burodi a jihar
Sun kuma yi wannan zaman ne a ranar Laraba, wanda a karshensa suka fitar da sanarwar cimma matsaya.
A sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin-Gado da kuma shugaban kungiyar masu yin burodin da sakatarensa, sun amince cewa, ba za su rage farashin burodin ba, maimakon haka sai dai su kara girmansa da ingancinsa.
Dukannin bangarorin biyu sun amince da wanan matsayar a cewar Uban kungiyar Alhaji Aminu Hassan a hirarsa da wakilinmu
“Baya ga fulawa, akwai wasu muhimman abubuwan da muke bukata wajen yin burodin wadanda farashinsu bai ragu ba, sai fulawa kadai, don haka ba’a bukatar rage farashin burodin….” Inji shi
Bukatar zaman na zuwa ne bayan da farashin burodin ya ki sauka a jihar Kano da sauran jihohi duk da cewa farashin buhun fulawa ya sauka zuwa Naira 60,000 daga sama da dubu 80,000
Kungiyar ta tabbatar da cewa daga yanzu za’a ga sauyi a burodin da jama’ar Kano ke saye ta bangaren girma da dandano sakamakon tattaunawar