Kamfanonin jiragen sama na ƙasashe daban-daban sun dakatar ko soke zirga-zirgarsu zuwa Riyadh, babban birnin Saudiyya, sakamakon rufe filin jirgin sama da kuma tabarbarewar yanayin tsaro.
Kamfanin jiragen sama na Kuwait Airways ya sanar da soke jiragensa biyu da aka shirya sauka a Riyadh.
Haka kuma, kamfanin Etihad Airways ya soke jirage da dama tsakanin Abu Dhabi da Riyadh har zuwa ranar Litinin, sakamakon rufe filin jirgin sama na King Khalid da ke birnin.
A nasa ɓangaren, kamfanin Air India ya tsawaita dakatar da zirga-zirgarsa zuwa Riyadh har zuwa ranar 15 ga Oktoba.
Sauran kamfanonin da suka dakatar da jiragensu zuwa Riyadh na wasu kwanaki sun haɗa da Flydubai, Turkish Airlines, Lufthansa da Pakistan International Airlines.
A wani mataki na daban, Hukumar Kula da Tsaron Jiragen Sama ta Tarayyar Turai ta faɗaɗa shawarwarinta kan amfani da sararin samaniyar Saudiyya, tana mai nuna damuwa kan ƙarfin mayakan Houthi na kai hare-hare zuwa wurare masu nisa a cikin ƙasar, musamman wuraren da suka shafi harkokin sufurin jiragen sama.
Kasashen Jamus, Kanada da Sifaniya su ma sun gargaɗi ’yan ƙasashensu da su guji tafiye-tafiye zuwa Riyadh, musamman ta filin jirgin saman King Khalid.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, ya zuwa lokacin tattara shi, shafin FlightRadar da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama ya nuna an soke jirage 297 a yankin.
