Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga iyaye, shugabanni da al’umma baki ɗaya da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen auren ƙananan yara tare da kare haƙƙoƙin ’ya’ya mata a Najeriya.
Ta bayyana hakan ne a saƙonta na bikin Ranar ’Yar Mace ta Duniya ta shekarar 2026, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Kawo ƙarshen auren yara da zuba jari wajen kare haƙƙoƙin ’ya’ya mata.”
Sanata Oluremi ta jaddada muhimmancin bai wa kowace yarinya damar samun ilimi, ingantaccen kiwon lafiya da kuma yanayin da zai ba ta damar cimma burinta a rayuwa.
Ta ce kowace yarinya na da haƙƙin yin karatu, girma da kuma gina makomarta ba tare da fuskantar wariya, cin zarafi ko wasu munanan al’adu da ke hana ta cimma burinta ba.
Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma yi kira ga iyalai, al’umma, shugabannin addinai da na gargajiya, da masu tsara manufofi da su ɗauki matakan kare haƙƙoƙin ’ya’ya mata tare da kawo ƙarshen auren ƙananan yara.
Ta bayyana cewa auren yara na hana ’ya’ya mata damar ci gaba da karatu da samun ingantacciyar rayuwa.
Sanata Oluremi ta ƙara da cewa bai wa ’ya’ya mata damar bunƙasa da cimma burinsu zai amfani iyalai, al’umma da ƙasa baki ɗaya.
