Yau Talata ake sa ran babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres zai je Islamabad, babban birnin Pakistan domin tattaunawa kan ƙoƙarin sasanta tsakanin Amurka da Iran.
Ana sa ran Guterres zai gana da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Fira Minista Shehbaz Sharif da Ministan Harkokin Waje Mohammad Ishaq Dar.
Wata Sanarwar ta ce ziyarar za ta kasance “damar tattauna rawar da Islamabad ke takawa cikin yanayi mai kyau wajen tallafa wa tattaunawar tsakanin ƙasashen biyu.”
Guterres ya kai ziyarar sa ta ƙarshe ne kasar a shekarar 2022, a lokacin da mummunar ambaliyar ruwa ta haddasa barna mai yawa a ƙasar.
