Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta bayyana cewa ta gano wata motar SUV da aka sace shekaru biyar da suka gabata a jihar Rivers.
Rahoton ya nuna cewa an gano motar ne ne bayan bincike da haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda aka bi diddigin bayanan laifin har aka gano motar a jihar Gombe.
Binciken ‘yan sanda ya kuma nuna cewa motar na daga cikin jerin motocin da ake zargin an saceta daga sassa daban-daban na ƙasar nan sannan aka kai su wasu jihohi domin amfani ko sayarwa ba bisa ka’ida ba.
Hukumomin ‘yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a wannan laifi tare da dawo da duk wasu kadarorin da aka sace.
Rundunar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da ƙoƙari wajen yaƙi da satar motoci da sauran laifuffuka a faɗin ƙasar.
