Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, kuma Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Kano, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, sakamakon rasuwar mai ɗakinsa.
Cikin wata sanarwar ta’aziyya da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga Farfesa Pakistan da iyalansa, tare da al’ummar Musulmi da duk masu hulɗa da marigayiyar.
Gwamnan ya ce marigayiyar ta yi rayuwa mai cike da ibada, tawali’u da tausayi, tare da sadaukar da kai wajen kyautata rayuwar iyali da al’umma.
Ya ƙara da cewa rasuwarta ta bar babban giɓi da za’a dade ana jin rashinta, musamman ga waɗanda suka amfana da shawarwari, hikima da kulawar uwa da take bayarwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na yin addu’ar Allah Ya gafartawa marigayiyar a madadin al’ummar Kano, tare rokon Allah ya baiwa Farfesa Pakistan da ‘ya’yansa da sauran iyalai juriyar rashin ta da aka yi.
