
Fadar shugaban kasar sudan da sojojin kasar suka sake kwacewa a ranar juma'a
Rundunar Sojin Sudan ta bayyana cewa ta sake ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum.
Magana da yawun sojojin kasar Nabil Abdallah ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin ɗin ƙasara ranar Juma’a bayan gwabza yaƙi da rundunar RSF babban birnin.
“Dakarunmu sun halaka abokan gabarmu da kayayyakinsu, da ƙwace ɗumbin kayayyakinsu da makamai,”
“Za mu ci gaba da samun nasara a duk fagagen daga har sai mun samu nasara baki ɗaya da kuma tabbatar da cewa an kawar da duk wasu mayaƙa da magoya bayansu daga ƙasarmu”. In ji Abdallah.

An ga sojojin kasar suna ta yaɗa bidiyoyi da ke nuna cewa suna cikin fadar shugaban kasa, inda suke taya juna murna a shafukan sada zumunta,
TRT ta rawaito cewa Ƙungiyar RSF ta ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar a Afrilun 2023, bayan yaƙi ya ɓarke tsakaninsu da sojoji, a inda suka yi saurin ƙwace iko da titunan Khartoum tare da tilasta wa sojojin tsere wa zuwa Port Sudan da ke gaɓar Bahar Maliya.
Tsakiyar birnin Khartoum nan ne inda fadar shugaban ƙasa tare da sauran ma’aikatu suke da manyan ma’aikatu, ya kuma kasance fagen yaki tsakanin sojojin da dakarun RSF.
A cikin kusan shekara biyu da aka shafe ana rikici tsakanin ɓangarorin biyu, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da raba fiye da mutum miliyan 12 da muhallansu.