Jiragen sojin Saman Najeriya sun yi luguden wuta tare da halaka ‘yan bindigan da aka fi sani da Lakurawa da yawa yayin da suke shirin kai wa fararen hula hari.
Mayaƙan sun gamu da ajalinsu ne a yankin Zangeku na Jihar Zamfara da ke iyaka da Jihar Kebbi.
Haka kuma wasu ’yan bindiga daga gungun ɗan ta’adda Ado Aleiro sun mutu a yayin luguden wutan da jiragen soji suka yi wa sansanoninsu.
Kakakin Rundunar Sojin Saman kasar nan, Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce sojin ta samu nasarar halaka su ne bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar su.
Sakamaon haka mutane da yama da aka yi garkuwa da su kubuta daga sansanin ’yan bindigar a yayin harin.
Mayaƙan da ake zargin cewa daga ƙasashen waje suka shigo kasar sun addabi yankunan Sakkwato da Kebbi da kisan jama’a da kuma satan dabbobi.
Kuma Hedikwatar Tsaron ta tabbatar ta na yin duk mai yiwu wa domin murƙushe su.