Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayen iskar gas...

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayen iskar gas daga Najeriya

Date:

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayen iskar gas daga Najeriya da nufin cike gibin makamashi da kasarsa ke fama shi tun bayan raba gari da Rasha sakamakon mamaye Ukraine da ta yi.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki daya kai lagos da Accra inda ya bayyana cewa gwamnatin jamus na shirin hada hannu wajen bullo da wata sabuwar hanya samun sinadarin hydrogen wanda ke samar da iskar gas.

Wannan shi ne karo na 3 da shugaban gwamnatin Jamus ke kai ziyara a kasashen Afirka a kokarin fadada alakar kasarsa tun bayan zama shugaban gwamnatin kasa da shekaru biyun da suka gabata.

Masana tattalin arziki naganin wannan wata hanya ce da zata karawa kasar nan hanyoyin kudin shiga da kimiya a siyasar duniya.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...