Jigo a jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna halin ko-in-kula da ɗaliban da aka sace a jihar Borno.
Galadima, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da Jam’iyyar NDC ta shirya a Maiduguri.
Ya ce sace ɗalibai a yankunan Mussa da Lassa, tare da rashin ɗaukar matakin gaggawa na ceto su, na nuna cewa gwamnatin Tinubu ba ta bai wa Borno muhimmanci kamar sauran jihohi ba.
Ya kwatanta lamarin da sace wasu ɗalibai a Jihar Oyo, inda ya ce Shugaba Tinubu ya tura shugabannin hukumomin tsaro domin tabbatar da an ceto su.
Ya ƙara da cewa duk da kasancewar Borno na da mataimakin shugaban ƙasa, Gwamnatin Tarayya ta fi mayar da hankali kan ceto ɗaliban Oyo, yayin da ta yi watsi da waɗanda aka sace a Borno.
Buba Galadima, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto ɗaliban Borno.
