Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya musanta bayar da umarnin kama masu goyon bayan jam’iyyun adawa ko mutanen da ke sukar gwamnatinsa.
Zulum ya bayyana hakan ne a Maiduguri ranar Juma’a, inda ya ce ya yi matuƙar mamakin rahotannin da ke danganta gwamnatinsa da kamen wasu mutane da ’yan sanda suka yi bisa zargin sanya rigunan da ke ɗauke da saƙon “Tinubu Must Go”.
Gwamnan ya ce bai san da kamen mutanen ba, kuma bai bayar da umarnin kama ko tsare su ba.
Ya jaddada cewa babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai shi ne dawo da zaman lafiya da sake gina jihar bayan shafe shekaru ana fama da hare-haren Boko Haram, ba wai kama abokan hamayyar siyasa ba.
A cewarsa, ya sha jefa kansa cikin haɗari domin kare al’ummar jihar, ciki har da mambobin jam’iyyun adawa, tare da tabbatar da zaman lafiya a Borno.
Zulum ya kuma tambayi dalilin da zai sa ya bayar da umarnin kama wani saboda bambancin ra’ayin siyasa, yana mai cewa Jihar Borno ta kasance tungar jam’iyyar APC sama da shekaru goma.
