Masarautar Sarkin Ginin Kano ta koka kan matakin gwamnatin jihar Kano na karɓe ikon gudanar da ayyukan gyaran gine-ginen wuraren tarihi na Kano, tana mai cewa hakan ya tauye musu aikin da suka gada daga iyaye da kakanninsu.
Wakilin Sarkin Ginin Kano, Alhaji Ali Sabo Yakasai, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da fadar masarautar ta kira.
Ya ce masarautar na kallon yadda ake karɓe musu wannan aiki da suka gada tun kaka da kakanni, musamman ayyukan gyaran Ganuwar Kano da ƙofofinta na tarihi, gidan Ɗan Hausa, katangar gidan sarki da sauran tsofaffin gine-ginen tarihi.
Alhaji Ali Sabo Yakasai ya kuma bayyana cewa kakansu, Zakari Ya’u, shi ne ya gina gidan Ɗan Hausa a tsakanin shekarar 1905 zuwa 1907, yana mai cewa wannan na daga cikin tarihin da ke nuna irin rawar da iyalansu suka taka wajen kula da gine-ginen tarihi na Kano.
