Tsohon Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sanata Babafemi Ojudu, ya yi Allah-wadai da rahoton zargin jifan ayarin motocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Ojudu, wanda jigo ne a jam’iyyar APC, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Ya kuma nuna damuwa kan harin da aka ruwaito an kai wa magoya bayan jam’iyyar NDC yayin wani taron siyasa a Legas.
Ojudu ya ce duk da bambancin waɗannan al’amura, suna nuna buƙatar ɗaukar matakan daƙile tashin hankali a harkokin siyasar Najeriya.
Sanatan ya jaddada cewa wajibi ne a tabbatar da tsaron shugaban ƙasa da sauran ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayinsu na siyasa ba.
