
Aminu Abdullahi Ibrahim
Isra’ilawa na gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru uku da harin Hamas da aka kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba 2023.
Ana gudanar da bukukuwan ne cikin yanayin jimami ga waɗanda suka mutu da kuma tunawa da mutanen da aka yi garkuwa da su.
Harin na 2023 ya haifar da yakin da ya janyo babbar asarar rayuka da lalacewar ababen more rayuwa a Gaza.
A Isra’ila, iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda aka yi garkuwa da su na ci gaba da neman amsoshi da ƙarin bayani kan makomar waɗanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.
BBC ta ruwaito cewa bikin na bana na faruwa ne yayin da siyasar Isra’ila ke fuskantar muhawara mai ƙarfi gabanin zaɓe.
A Gaza kuwa, ana ci gaba da fuskantar matsanancin tasirin yakin, yayin da al’amuran jin ƙai, gidaje, asibitoci da makarantu ke ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali.
