Babbar kotun tarayya da ke Kano ta Sanya ranar 19 ga Disamba domin yake hukinci kan karar da Dan takarar gwamnan Kan a jam’iyyar PDP Sadiq Wali ya shigar na kalubalantar Jaafar Sani Bello da ya shiga cikin kararsa.
Idan za a iya tunawa Jaafar Sani Bello ya shigar da karar Muhammad Abacha, da jamiyyar PDP da kuma INEC gaban kotu don neman a kwace takarar Muhammad Abacha.
Ya shigar da karar ne kan zargin cewa Muhammad Abacha ba ma dan jamiyyar PDP ba ne.
Sai dai bayan da aka tabbatar da Sadiq Wali a matsayin halastaccen Dan takara ne, Jaafar din ya nemi ya shiga cikin karar ta Sadiq Wali akan Muhammad Abacha wanda kuma kotun tarayya ta Amince da Hakan.
Mai shari’a Aminu Liman ya Sanya ranar 19 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan shari’ar.
A baya dai an sanya ranar yau Alhamis a matsayin ranar da za a yanke hukunci kan shari’ar Amma saboda yanayin tsaro ya dage hukincin.