Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa rikice-rikice da saɓanin da ke cikin jam’iyyar APC sun fi ba shi damuwa fiye da ’yan adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da hedikwatar yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wadda ke fafutukar ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shi a zaɓen 2027.
Ya ce ba ya fargabar jam’iyyar PDP ko tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, amma abin da ya fi damunsa shi ne saɓani da rashin haɗin kai a cikin APC.
A kalamansa, ya ce idan ’yan jam’iyyar suka haɗa kai kamar iyali ɗaya, za su iya samun nasara a zaɓen da ke tafe.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma gargaɗi shugabannin APC a Arewa da su guji goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, alhali suna yi wa gwamnonin jam’iyyar zagon ƙasa a zaɓen gwamna.
Ya buƙaci ’yan jam’iyyar da su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Tinubu, gwamnonin APC da ’yan majalisun dokoki baya domin samun nasara a zaɓen 2027.
