Akalla mutane biyar ne suka mutu bayan wata tankar dizal mai ɗauke da lita 45,000 ta yi hatsari tare da murƙushe motoci da dama a kan hanyar Iwo road zuwa Ojoo, a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, a tashar motoci ta Aduloju, gaban ginin Dominion City. Motocin da hatsarin ya shafa sun haɗa da motocin haya ƙirar Nissan Micra.
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Oyo, OYRTMA, ta ce ana zargin tankar ta samu matsalar birki kafin ta faɗa kan ɗaya daga cikin motocin haya, mutanen biyar da suka mutu sun haɗa da maza biyu, ciki har da direban motar, da mata uku da ke cikin motar.
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda kwamishinan ’yan sanda, Abimbola Ayodeji Olugbenga, ya bayar da umarnin tura jami’ai domin gudanar da aikin ceto da tabbatar da tsaro a wurin. Jami’an ’yan sanda, hukumar FRSC da OYRTMA sun taimaka wajen kwashe tarkacen motocin da daidaita zirga-zirga. An kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin Adeoyo.
