Majalisar Wakilai ta tarayya na nazarin wani kudirin doka da ke neman kafa hukumar kula da kadarorin jama’a ta kasa, domin bibiyar kadarorin gwamnatin tarayya, tantance ƙimarsu da kuma kula da yadda ake sarrafa su.
Idan aka amince da kudirin, hukumar za ta kasance da alhakin gano kadarorin gwamnati da tantance darajarsu, tare da inganta tsarin kula da su.
Wannan mataki na zuwa ne a ƙoƙarin samar da ingantaccen tsari na kula da kadarorin gwamnati, da kuma taimakawa wajen tabbatar da cewa ana amfani da su yadda ya kamata.
