
Matatar Main Fetur na garin Haifa da harin Bom na Iran ya durkusar
Matatar Mai ta ƙasar Isra’ila da ke Haifa ta dakatar da ayyukanta gaba ɗaya, bayan wani harin roka da Iran ta kai ya yi mata barna.
Hukumar Gudanarwar Matatar, Bazan Group, ta bayyana cewa harin ya lalata tashar samar da wutar lantarki da matatar ke amfani da ita, lamarin da ya tilasta musu dakatar da dukkan ayyukansu.
Rahotanni daga hukumomin Isra’ila sun tabbatar da mutuwar wasu ma’aikata uku sakamakon harin cikin sabon rikicin da ke ƙara zafi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jerin hare-haren Iran na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bisa jerin hare-haren da Isra’ila ta kai a sassan Iran ciki har da birnin Tehran inda akalla mutane 220 suka mutu galibinsu mata da kuma ƙananan yara. Baya ga wasu manyan jami’an tsaro na kasar da kuma wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.
Isra’ila ta ce, hare-harenta na baya-bayan nan na da nufin hana Iran mallakar makaman nukiliya, lamarin da ta ce ka iya faruwa nan da shekara guda ko ma cikin ‘yan watanni masu zuwa.
A martaninta, gwamnatin Iran ta bayyana cewa Isra’ila za ta dandana kudar ta bisa hare-haren da ta kai wa fararen hula da cibiyoyin soji da tashoshin makamashin nukiliya.
Ya kuma ƙara da cewa, harin bai dakile shirinta na nukiliya ba domin samar da wutar lantarki da kuma sauran hanyoyin zaman lafiya.
Hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai sun shafi cibiyoyin soji, tashar wutar lantarki da matatun mai a Isra’ila, inda aka ruwaito mutuwar mutane fiye da 24, da rushe gine-gine a biranen Tel Aviv da kuma birnin Kudus.
Rikicin na ci gaba da haifar da damuwa a duniya, tare da kira daga kasashen duniya na neman da a dakatar da daukar fansa domin kauce wa rikicin da ka iya rikidewa ya zama yakin duniya.