27.9 C
Kano
Friday, July 26, 2024
HomeLabaraiRanar Hausawa

Ranar Hausawa

Date:

Al’ummar Hausawa na cikin al’ummomin da suka cuɗanya sosai da sauran ƙabilu masu maƙwabtaka ko hulɗar arziƙi da su a cikin ƙasashen Afirka ta Yamma da ɗaukacin nahiyar, har ma da duniya gaba ɗaya.

Ƙiyasi na baya-baya da aka yi cikin shekarun da suka wuce, a cewar Farfesa Muhammad Bunza, ya nuna Hausawa sun kai miliyan 150.

Amma dai masana na ganin cewa haƙiƙanin yawan Hausa ya yi matuƙar zarce haka.

Yau ne, ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake tunawa da ita duk rana irin ta yau, 26 ga watan Agusta.

Albarkacin wannan rana kuma, mun zanta da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, shahararren malami a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Malamin dai ya yi jawabi ne a kan muhimmancin ranar, da al’adu da asalin al’ummar Hausawa, har ma da ƙalubalen rayuwarsu.

Farfesa Bunza ya ce akwai ɗumbin Hausawa a ƙasashe masu nisa da ƙasar Hausa, kamar Saudiyya da Sudan da Moroko.

Kuma saboda yawan auratayya da kuma kasancewar Hausa, harshen da ke haɗa hulɗar ciniki da sauran mu’amalolin rayuwa ga mabambantan ƙabilu, a wasu lokuta har akan yi tababa shin ko akwai Bahaushen asali ma kuwa?

”Samun Bahaushe na asali wanda shi Bahaushe ne ɗan Bahaushe, jikan Bahaushe, kama kunnen Bahaushe uhuhum na Bahaushe babu shi”, in ji shehin malamin jami’ar.

Malamin ya ce dalili kuwa shi ne auratayya tsakanin Hausawa da sauran ƙabilu ya yi tasiri sosai wajen tantance Bahaushen asali.

“A yanzu idan ka samu mutum Bahaushe to watakila mahaifinsa ko kakansa kuma za ka samu wata ƙabilar ce daban ba Bahaushe ba”. in ji shi

Ya ce Hausawa sun mamayi wurare masu yawa a Afirka ta yamma da ma faɗin Afirka.

Farfesa Bunza ya ce Hausawa sun watsu wurare masu yawa a duniya, kuma wani abin da ke ƙara ƙarfafa su, shi ne duk inda suka je kansu a haɗe yake, suna tafiya da tsarinsu na shugabanci.

Shehin malamin ya ce akwai harsuna kusan 7500 a fadin duniya, kuma harshen Hausa shi ne na bakwai a yawam masu amfani da shi a fadin duniya.

Farfesa Bunza ya ce a ganinsa in dai za a haɗa masu magana da harshen Hausa amatsayin harshensu na biyu da wadanda ke magana da si a matsayin harshen uwa, to al’ummar Hausawa za su kai kusan miliyan 500.

“Mai musun haka ya je Moroko, ko ya shiga Libiya ko Mali da sauran ƙasashen duniya”.

Kalubalen da Harshen ke fuskanta

Farfesa Bunza ya ce baban ƙalubalen da harshen Hausa ke fuskanta shi ne samun kishi ga masu karatun Hausa.

Sannan a samu kishi ga daliban da ke karanta Hausa a jami’o’i.

Shehin malamin ya kuma yi kira ga hukumomi da su kula sosai wajen daga darajar harshen domin kuwa a cewarsa “kaf Afirka in ka cire harshen Swahili babu harshen da zai iya yin gaba da gaba da harshen Hausa’

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...