Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa za ta ɗauki nauyin kula da iyalan Ummulkhair, malamar makarantar Islamiyya da aka hallaka a yankin Maraban Jos da ke ƙaramar hukumar Igabi.
Gwamnan jihar, Uba Sani, ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, inda ya jajanta musu kan wannan mummunan lamari.
Ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa an yi adalci, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin ganin waɗanda ake zargi da hannu a kisan sun fuskanci hukunci bisa doka.
Haka kuma ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta tallafa wa iyalan marigayiyar domin rage musu radadin wannan rashi.
Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai jaddada cewa duk wani zargi ya kamata a miƙa wa jami’an tsaro domin gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.
