Wani sabon bincike da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ya nuna cewa sama da mutane biliyan 1.17 ne suke rayuwa da matsalolin tabin hankali a shekarar 2023, inda aka samu karin kaso 95.5 cikin 100 tun daga shekarar 1990.
Masu binciken daga cibiyar Institute for Health Metrics and Evaluation sun ce cututtukan damuwa da fargaba su ne suka fi yawaita a duniya.
Rahoton ya nuna cewa masu fama da matsalar damuwa sun karu daga miliyan 182 a 1990 zuwa miliyan 470 a 2023, yayin da masu fama da matsanancin bakin ciki suka karu daga miliyan 102 zuwa miliyan 236.
Binciken ya kuma bayyana cewa mata sun fi fuskantar matsalolin tabin hankali idan aka kwatanta da maza, yayin da cututtuka irin su autism da ADHD suka fi yawa a tsakanin maza.
Masu binciken sun ce matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19 su ne suka fi shiga hadarin kamuwa da matsalolin tabin hankali saboda muhimmancin wannan lokaci wajen ci gaban kwakwalwa da rayuwa.
Rahoton ya kuma danganta annobar COVID-19 da karuwar matsalolin damuwa da fargaba, yana mai cewa har yanzu wasu daga cikin matsalolin ba su koma yadda suke kafin annobar ba.
Masu binciken sun bukaci kasashe musamman masu karamin karfi da matsakaicin tattalin arziki da su kara inganta tsarin kula da lafiyar kwakwalwa tare da samar da hanyoyin kariya da magani tun da wuri.
