Yayin da Najeriya ke shiga kololuwar daminar bana, hukumomin lafiya na fuskantar sabon ƙalubale mai hatsari—barkewar cutar kwalara da ke ci gaba da yaduwa a wasu jihohin Arewacin ƙasar, inda ta riga ta hallaka mutane tare da jikkata dubban jama’a.
A jihohin Borno da Plateau, rahotanni sun nuna cewa cutar ta fi kamari a sansanonin ‘yan gudun hijira da wasu yankunan karkara, yayin da sauran jihohi ke ƙara tsaurara matakan sa ido domin hana yaduwar ta.
Masana lafiya sun ce matsalar na da alaƙa da ƙarancin ruwan sha mai tsafta, rashin ingantaccen tsaftar muhalli da kuma cunkoson jama’a musamman a sansanonin gudun hijira.
Borno: Cutar na kara kamari a sansanonin ‘yan gudun hijira
A jihar Borno, rahotanni daga ƙungiyar likitoci masu zaman kansu Médecins Sans Frontières (MSF) suka nuna cewa an samu mummunan bullar cutar, inda aka samu dubban sabbin kamuwa da cikin ‘yan makonni.
Rahoton MSF ya ce an samu mutuwar mutane 74 da kuma sabbin mutane 7,850 da ake zargi sun kamu da cutar tsakanin farkon watan Mayu zuwa 9 ga Yuni.
Haka kuma, an bayyana cewa a cikin mako guda, jihar ta samu mutuwar mutane 35 da sabbin masu cutar 3,646, lamarin da ya sa ma’aikatan lafiya ke aiki cikin matsanancin hali.
Wani ma’aikacin lafiya a Maiduguri ya ce, “Cibiyoyin kula da masu cutar sun cika fiye da kima, kuma kowace rana ana samun sabbin marasa lafiya da yawa fiye da yadda ake tsammani.”
Monguno: 296 sabbin masu cutar cikin kwana uku
A sansanin ‘yan gudun hijira na Monguno, lamarin ya ƙara ta’azzara inda aka samu mutane 296 da ake zargin sun kamu da cutar cikin kwanaki uku kacal.
Rahotanni sun nuna cewa an samu 48 a ranar 11 ga Yuni, 68 a ranar 12, sannan kuma 180 a ranar 13 ga watan.
Wani ma’aikacin lafiya ya ce yawancin wadanda suka kamu mata da yara ne daga sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ya ce, “Yawancin marasa lafiya suna zuwa a makare, wasu ma sun fara jinya a gida har cutar ta tsananta kafin su kawo kansu asibiti.”
Wata mazauniyar yankin, Yagana Lawan, ta bayyana yadda ɗanta ya kamu da cutar cikin gaggawa.
“Nan take ya fara amai, daga baya kuma zawo mai tsanani. Mun garzaya da shi asibiti daga nan aka tura mu cibiyar kula da kwalara,” in ji ta.
Plateau: An tabbatar da mutuwar mutum 5
A jihar Plateau kuwa, Kwamishinan Lafiya, Dakta Nicholas Baamlong, ya tabbatar da cewa mutane biyar sun mutu, yayin da aka samu 52 da ake zargin sun kamu da cutar a karamar hukumar Mangu.
Ya ce yankunan da abin ya shafa sun hada da Pushit, Mangu I da Mangu II, yana mai cewa ana kokarin shawo kan lamarin kafin ya kara bazuwa.
“Mun dauki lamarin da matuƙar muhimmanci domin hana yaduwar cutar zuwa wasu yankuna,” in ji kwamishinan.
Kira ga matakan gaggawa
Masana lafiya sun gargadi cewa idan ba a dauki matakan kariya cikin gaggawa ba, cutar na iya yaduwa zuwa wasu jihohi a cikin makonni masu zuwa, musamman yayin da damina ke kara tsananta.
Sun kuma jaddada bukatar inganta ruwan sha, tsaftar muhalli da kuma wayar da kan jama’a domin dakile yaduwar cutar.
