Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNLO 2024: Kungiyar Barau FC ta kafa tarihi bayan tsallakawa zuwa gasar...

NLO 2024: Kungiyar Barau FC ta kafa tarihi bayan tsallakawa zuwa gasar NNL

Date:

Kungiyar Kwallon kafa ta Barau Football Club ta samu tikitin buga gasar Firimiyar Najeriya mai daraja ta biyu wato NNL, bayan nasarar data samu kan Yoca Crocodiles da ci 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaran raga.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Ahmad Hamisu Gwale, ya sanyawa hannu ta rawaito Barau ta fafata wasan ne a ranar Lahadi a filin wasa na FIFA Goal Project da Ke birnin Tarayya Abuja.

Da fari dan wasan gaba na Yoca Crocodiles Sani Dan Bauchi ne ya fara zura kwallo a minti na10 Da fara wasan, kafin Auwal Muhammed ya warwarewa Barau FC a minti na 60 kuma haka aka tashi a wasan.

Sai dai kungiyar Maliya Boy’s ta samu tikitin buga gasar ta NNL bayan samun nasara a bugun daga kai sai mai tsaran raga bayan Kyaftin Salem Ali ya zura kwallo data bawa Barau FC nasara.

Barau FC karkashin Shugaban ta Alhaji Ibrahim Shitu Chanji a karon farko a tarihi kungiyar ta samu tikitin buga gasar ta NNL sakamakon nasara akan Yoca Crocodiles daga jihar Kaduna.

Kungiyar dai nasamun kulawa da kuma goyan bayan jagoranta Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Jibrin wanda ke daukar nauyin duka lamuran kungiyar.

A nasa jawabin mai horar da kungiyar ta Barau FC Madu Muhammad ya bayyana godiyarsa ga Allah da wannan nasara da ya jagoranci kungiyar ta samu akan Yoca Crocodiles.

“Samun nasara zuwa gasar Firimiyar Najeriya mai daraja ta biyu ba abune mai sauki ba, amma gashi munyi nasara muna yiwa Allah godiya da wannan nasara da ya bamu”

“Insha Allah, da goyan bayan da muke samu daga kowanne bangare zamu ci gaba da yin aiki tukuru domin bawa marada kunya,” a cewar Madu Muhammad.

Kawo yanzu haka dai kungiyar Kwallon kafa ta Barau FC ta kafa tarihin buga gasar Firimiyar Najeriya mai daraja ta biyu NNL bayan da a baya ba iya samun wata kungiya daga jihar Kano data kafa tarihin zuwa wannan mataki.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...