Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta ce aikin shigar da bayanan ’yan takararta ne ya janyo rashin ganin sunan ɗan takararta na gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a cikin jerin sunayen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Hussaini Isa Mairiga, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Premier Radio a daren jiya.
Mairiga ya bayyana cewa ana kan aikin shigar da bayanan ’yan takarar jam’iyyar ne, wanda hakan ya sa ba a ga sunan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a jerin sunayen da hukumar INEC ta fitar ba.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilin Premier Radio, Musapha Muhammad Kankarofi.
Tun da farko, hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna a Jihar Kano, inda ba a ga sunan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ba.
Haka kuma, hukumar ta cire sunan Farfesa Isa Ali Pantami daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna a Jihar Gombe, duk da cewa ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP.
Sai dai INEC ba ta bayyana dalilin rashin saka sunayen ’yan takarar biyu a cikin jerin sunayen da ta fitar ba.
