Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Jordan sun kulla sabon yarjejeniyar fahimtar juna domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da musayar bayanan sirri.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Amman na Jordan, inda Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro na Najeriya, Dr Bello Matawalle, da Shugaban Hafsoshin Sojin Jordan, Manjo Janar Yousef A. Alhnaity suka halarta.
Yarjejeniyar na da manufar inganta hadin kai tsakanin kasashen biyu a fannoni kamar yaki da ta’addanci, horar da jami’an tsaro, binciken harkokin tsaro da musayar bayanan sirri.
Haka kuma, bangarorin biyu sun amince da kara hadin gwiwa wajen bunkasa fasahar tsaro da kuma kafa hanyoyin musayar kwarewa tsakanin sojojin kasashen.
Ministan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin muhimmiyar dama da za ta kara karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Jordan, musamman a wannan lokaci da kalubalen tsaro ke karuwa a duniya.
Ya kara da cewa hadin gwiwar zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna daban-daban.
Daga Buhari Garkuwan Fazbuk
