Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaMutane 6 sun bace a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Mutane 6 sun bace a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Date:

Karibullahi Namadobi

 

Hukumomi sun gano gawar mutum 16, yayin da wasu shida kuma suka bace, sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Karamar Hukumar Koko/Besse a Jihar Kebbi.

 

Gwamnan jihar, Atiku Bagudu da Ministan Shari’a Abubakar Malami sun kai ziyarar jaje yankin don nuna alhininsu game da faruwar lamarin.

 

Bagudu ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu tare da bai wa iyalansu hakurin rashinsu.

 

Gwamnan ya kuma yaba wa wadanda suka sadaukar da lokacinsu don aikin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.

 

Sannan ya gargadi masu jiragen ruwa da guje wa tafiyar dare da kuma yin lodi da ya wuce kima tare da kuma daukar matakan kariya.

Latest stories

Related stories