Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya dora alhakin karancin wutar lantarki a kasar nan kan matsalar tsaro da aka fuskanta a 2024 da ta gabata.
A sakonsa na sabuwar shekara da mashawarcinsa kan sadarwa Bolaji Tunji ya fitar, ministan ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake yawan kai hare-hare da barnata turakun wutar lantarki.
Ya danganta harin da ake kai wa akai-akai, da ya ce ya yi illa ga karuwar samar da wutar lantarki ga gidaje da yan kasuwa.
A cewarsa, babban abinda ya kawo cikas ga samun nasarar samar da wutar lantarki a kasar nan a shekarar da ta gabata, shi ne, hannun wasu yan kasa marasa kishin, da ya bayyana a matsayin yan bindiga.
Ya bukaci yan Najeriya da su nuna kishin kasa a duk lamuransu musamman kan kadarorin gwamnati.