31.9 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiMasu zanga-zanga sun hana shari'ar Mua'az Magaji

Masu zanga-zanga sun hana shari’ar Mua’az Magaji

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Masu zanga-zanga sun kawo wa zaman kotu cikas yayin da take ƙoƙarin ci gaba da sauraron ƙarar Mu’azu Magaji (Win Win) kan zargin cin zarafin Gwamna Ganduje da iyalansa.

Jami’an kotun da ke Nomans Land, Sabon Gari a nan Kano na cewa ba za su fara sauraron ƙarar ba har sai ‘yan zanga-zangar sun bar wurin.

Matasa ɗauke da kwalaye da ke nuna goyon baya ga tsohon kwamashinan na ayyuka sun yi cincirundo a bakin kotun, inda suke nema asaki Mu’azu Magajin.

A cewarsu tsare Ma’azu Magaji tamakar tauye masa hakkinsa ne da ya kamata a ce yana sararawa a cikin jama’a.

A wani bangaren kuma wasu matasan ne sauke da kwalaye da ke nuna bukatar a hukuntashi.

Matasan dai da suka yi ikirarin cewa su dalibai ne sun ce ba za su amince da cin zarafin gwamnan da Dansarauniya ke yi ba.

A don hakan ne ma suke bukatar kotu da ta tabbatar ta hukunta shi domi ya zama izina ga yan gaba.

Latest stories