Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya mai kula da harkokin man fetur ya yi watsi da ƙorafin da aka shigar kan mataimakin babban shugaban kamfanin NNPCL mai kula da harkokin rarraba man fetur, Dakta Mumuni Dagazau, bisa zargin halatta kuɗin haram da cin karo da muradun aiki.
Shugaban kwamitin, Ikenga Ugochinyere, ya bayyana hakan a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, bayan nazarin rahoton binciken da wani ƙaramin kwamiti ya gudanar kan zarge-zargen.
A cewarsa, waɗanda suka shigar da ƙorafin sun kasa gabatar da ƙwararan hujjoji da za su tabbatar da zargin, duk da damar da aka ba su.
Ya ce masu ƙorafin sun gabatar da rahotannin jaridu ne kawai a matsayin hujja, sannan suka ƙi komawa gaban kwamitin domin bayar da ƙarin bayanai.
Sai dai Dagazau ya amsa gayyatar kwamitin ta hannun wakilansa, waɗanda suka bayar da amsoshi kan tambayoyin da aka yi musu.
Ugochinyere ya jaddada cewa majalisar ba za ta yi hukunci kan zargi ba tare da sahihan hujjoji ba, yana mai cewa kwamitin zai ci gaba da bincikar duk wani ƙorafi da aka gabatar tare da gamsassun shaidu.
Kwamitin ya kuma bayyana goyon bayansa ga sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mahukuntan NNPCL ke aiwatarwa a ɓangaren man fetur.
