Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar da zata baiwa gwamnatin jihar damar samar da rundunar ‘yan sanda mallakin ta.
Shugaban masu rinjaye a majalisar Lawan Hussaini Dala ya ce, majalisar ta samar da dokar ne, biyo bayan amincewa da tayi da sauye-sauyen da majalisar wakilan Najeriya ta yi, domin baiwa jihohi damar kafa rundunar ’yan sandan su.
A wani ci gaba kuma, Majalisar ta amince da Kudirin rage Kasafin KuɗinJihar Kano na shekarar 2026, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar domin yin wasu gyare-gyare ga kasafin kuɗin jihar.
Tunda farko, an ware kimanin tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari huɗu da saba’in da bakwai a matsayin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026, sai dai Majalisar ta ce raguwar kuɗaɗen da jihar ke samu daga Asusun Tarayya sakamakon sauye-sauyen dokar haraji ya sanya aka buƙaci a rage girman kasafin.
Binta Khalid Muhammad ta rawaito cewa an rage kasafin kuɗin daga tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari huɗu da saba’in da bakwai zuwa tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari biyu da ashirin da biyu, wanda Majalisar ta amince da shi domin ya dace da halin da ake ciki na samun kuɗaɗen shiga na jihar.
