Majalisar dokokin jihar Legas ta nuna goyon baya ga shirin kafa rundunar ’yan sandan jiha, amma ta buƙaci a fayyace yadda za’a raba iko da nauyin ayyuka tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi a cikin kundin tsarin mulki.
Majalisar ta jaddada muhimmancin samar da ƙa’idoji bayyanannu da za su tsara ayyukan rundunar, tare da fayyace iyakokin ikon kowace gwamnati.
Wannan na zuwa ne yayin da majalisun dokokin jihohi ke nazarin kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa ’yan sandan jiha.
