Wasu mafarauta da aka fi sani da ’yanbula sun kashe wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane, tare da kwato kuɗin fansa naira miliyan 10 a dajin Falgore, da ke ƙaramar hukumar Doguwa.
Rundunar ’yan sandan Kano ta bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan masu garkuwar sun karɓi kuɗin fansar wani mutum mai shekaru 45, mai suna Kabiru Aliyu, wanda aka sace a yankin Falgore a watan Satumba, sannan suka sake shi ba tare da wata illa ba.
A cewar rundunar, mutane uku da ake zargin ’yan bindiga ne sun fito daga cikin dajin tsakar dare domin karɓar kuɗin. Bayan sun karɓi kuɗin tare da sakin wanda aka yi garkuwa da shi, mafarautan suka yi musu kwanton bauna yayin da suke komawa mafakarsu.
A yayin artabun, an kashe biyu daga cikin waɗanda ake zargin, yayin da na ukun ya tsere da raunuka. Rundunar ta ce an gano cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe mai suna Dogo Isah ne, ɗan asalin ƙauyen Maigwanda da ke ƙaramar hukumar Kubau ta jihar Kaduna. An kuma kwato kuɗin fansar naira miliyan 10.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa mafarautan bisa taimakonsu wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci. Ya kuma umarci jami’an tsaro da su ƙara bincike a dajin da yankunan da ke kewaye domin kamo wanda ya tsere.
Rundunar ta tabbatar da cewa an duba lafiyar Kabiru Aliyu tare da haɗa shi da iyalansa. A nata ɓangaren, rundunar sojin Najeriya ta ce sojoji tare da ’yan sanda, DSS da mafarauta ne suka gudanar da aikin haɗin gwiwa da ya kai ga ceto mutumin da kuma kwato kuɗin fansar.
