Ma’aikatan gwamnati a ƙarƙashin kungiyar haɗin gwiwar majalisar rattaunawa da ma’aikatan gwamnati ta kasa (JNPSNC) sun yi barazanar fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki uku daga ranar 2 ga Oktoba, idan gwamnatin tarayya ta gaza biyan buƙatunsu kafin wa’adin da suka bayar na 30 ga Satumba, 2026.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta riga ta shirya ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar domin shiga yajin aikin, idan gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace kan matsalolin da suka shafi jin daɗin ma’aikata da tsadar rayuwa ba.
Daga cikin buƙatunsu akwai rage farashin litar man fetur zuwa naira 500, biyan ma’aikata tallafin albashi na musamman domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa, da kuma kafa kwamitin haɗin gwiwa da zai fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi da ake sa ran zai fara aiki a shekarar 2027.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyin rage kuɗin shigo da man fetur, tare da tabbatar da samar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai domin ƙara tace mai a cikin gida da rage farashin man fetur.
A cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Olowoyo Gbenga, ya fitar, ya ce wa’adin 30 ga Satumba ya tsaya daram, yana mai kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi magana kan buƙatun ma’aikatan a jawabin da zai gabatar na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki kafin wa’adin, za ta fara yajin aikin gargaɗin a ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, domin matsa mata lamba ta biya buƙatun ma’aikatan.
