Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, domin yanke matsaya kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar game da cire sunayen wasu ’yan takara daga jerin masu neman muƙamai a zaɓen 2027.
Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai Farfesa Isa Ali Pantami na jam’iyyar PDP a jihar Gombe, da Abdulsalam Gwarzo na jam’iyyar NDC a jihar Kano, da kuma Sanata Danjuma Laah a jihar Kaduna.
Sauran sun haɗa da Sebastine Hon na jam’iyyar SDP a jihar Binuwai, Ladi Adebutu na PDP a Ogun, da Esson Mairiga na PDP a jihar Nasarawa.
Jam’iyyun PDP da SDP sun nuna rashin amincewarsu da cire sunayen wasu daga cikin ’yan takararsu, inda suka ce matakin kuskure ne da ya kamata hukumar zaɓen ta gyara.
Rahotanni sun bayyana cewa INEC ta kammala nazarin farko kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata, yayin da ake jiran matakin ƙarshe da za ta ɗauka.
Ana sa ran hukuncin hukumar na ranar Alhamis zai fayyace makomar ’yan takarar da sunayensu suka ɓace daga jerin sunayen da aka wallafa gabanin zaɓen 2027.
