Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sauya sunan Babban Asibitin Dawakin Tofa zuwa Dr Mahmud Baffa Yola General Hospital, domin girmama marigayin bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Gwamna Abba ya ce an dauki matakin ne domin adana tarihin marigayin, wanda ya yi fice a harkokin siyasa da gudanarwa tare da bada gagarumar gudunmawa ga hidimar jama’a a jihar Kano.
Gwamnan ya ce marigayin na daga cikin wadanda suka assasa tsarin ilimin manya a Kano, kafin daga bisani gwamnatin Marigayi Abubakar Rimi ta fadada shi, sannan shi ne ya jagoranci gangamin tara kudi daga al’umma a shekarar 1989, lamarin da ya haifar da kafa asibitin a garin Dawakin Tofa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na umartar Ma’aikatar Lafiya ta jihar da ta gaggauta fara aiwatar da aikin gyaran asibitin, tare da tantance irin kayan aikin lafiya da ake bukata domin inganta ayyukan jinya.
