Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan yadda take tafiyar da matsalolin tsaro da talauci a kasar nan.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Jos, a wani taro da ƙungiyar matasan Middle Belt ta shirya domin tikitin Peter Obi da Kwankwaso.
Ya ce gwamnatin da ta gaza kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da inganta walwalarsu, hakan bata cancanci sake samun wa’adin mulki ba.
Tsohon gwamnan Kano ya koka kan yadda hare-haren ’yan bindiga, Boko Haram da rikice-rikicen al’umma ke haddasa asarar rayuka, yana mai cewa dole ne kasar nan ta samu shugabannin da zasu kare rayukan al’umma ba tare da la’akari da addininsa ko ƙabilarsa ba.
Haka kuma, ya ce rashin masana’antu da ayyukan yi na ƙara ta’azzara talauci, inda ya jaddada buƙatar gwamnati ta zuba jari a fannin noma da ilimi tare da yaƙi da jahilci.
Kwankwaso ya bayyana tikitin Obi da shi a matsayin wanda zai haɗa kan ’yan Najeriya, yana mai cewa sun haɗa manufofinsu domin samar da shugabanci mai inganci.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Filato su zaɓi ’yan takarar NDC a zaɓen 2027, tare da kare ƙuri’unsu.
