
Aminu Abdullahi Ibrahim
Aƙalla ɗalibai 135 masu lalurar gani ne suka rubuta Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta 2026 (UTME) na Hukumar JAMB a Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shirin ya cika shekaru 10 da ba wa ɗalibai masu bukata ta musamman damar rubuta jarrabawar tun daga shekarar 2017.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan fara jarrabawar, Koodinetan cibiyar Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya bayyana cewa adadin ya kai fiye da kashi 25 cikin 100 na ɗaliban da ke da buƙatu na musamman a fadin kasar nan.
Turkiyya za ta ba jami’an tsaron Najeriya 200 horo na musamman.
Ya ce cibiyar Kano, wadda aka kafa tun 2017, tana karɓar ɗalibai daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna da Zamfara.
Farfesa Bello, tsohon Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya ƙara da cewa JAMB ta samar da masauki kyauta, abinci da tallafin sufuri ga ɗaliban a lokacin jarrabawar.

A bana dai, sama da ɗalibai 530 masu bukata ta musamman ne za suka rubuta jarrabawar JAMB a cibiyoyi 11 da hukumar ta ware a faɗin ƙasa.
Ya ce cibiyar dake Kano itace tafi kowacce yawan dalibai inda a yanzu dalibai 135 ne zasu rubuta jarabawa a cibiyar.
Ya kara da cewa dalibai masu bukata ta musamman sun fi samun nasara a jarabawar fiye da dalibai da suke yi a CBT.

Farfesa Bello, ya ce shigo da wannan tsarin jarabawa da Farfesa Ishaq Oloyede, babban cigaba ne kuma JAMB tana kashe kudi masu yawa wajen gudanar da ita.
Ya ce ana basu gurin kwana da abincin safe da na rana kuma za a basu wasu kudin na rage musu kudin moto da zasu koma gida.
